SHIN ZA'A IYA KAMUWA DA CUTAR CORONA VIRUS TA HANYAR JIMA'I

Idan na yi saduwa zan kamu da coronavirus? Babu mamaki kun yi wannan tunanin amma kuna kunyar tambaya.
Don bambance gaskiya da karya, mun mika tambayoyinku ga kwararru.
Dakta Alex George likita ne a bangaren kula ta gaggawa kuma tsohon tauraro a shirin Love Island. Alix Foz dan jarida ne a bangaren jima'I kuma tsohon mai gabatar da shirin Unexpected Fluids a tashar BBC Radio 1.
Babu damuwa idan aka yi tarawa lokacin annobar coronavirus?
Dr Alex George: Idan kana da aure kuma a gida daya kuke zaune babu damuwa. Amma idan wani daga cikinku na nuna alamomin coronavirus to dole ne ku rika barin tazara ko kuma ku killace kanku a cikin gidanku. Yadda ya kamata shi ne a bar tazarar mita biyu- ko a cikin gidanka amma muna ganin hakan ba zai yiwu ba.
Alix Fox: Idan kana jin alamun coronavirus kadan-kadan, yana da maatukar muhimmanci kar ka yi zaton abokin zamanka (wato matarka ko mijinki) ma na fuskantar haka. Don haka, idan kana jin alamu ko yaya, ka bar tazara tsakaninka da su.


  Yin jima'i da wasu mutanen na daban fa?
Dr Alex: Ba zan ba da shawarar yin sabbin abokan tarawa ba, saboda hadarin kamuwa da cutar.
Alix Fox: Haka kuma kar ku manta, wasu mutanen da ke dauke da cutar ba sa jin alamunta. Don haka ko kuna jin kanku kalau, kuna iya shafa wa wasu cutar kuma su ma suna iya shafa wa wasu ta hanyar mu'amala da su ko sumbatarsu.
Na sumbaci wani da na hadu da shi kwanan nan kuma daga baya ya fara nuna alamun cutar. Yayazan yi?
Dr Alex: Idan kun sumbaci wani ko kun yi mu'amala da wani da kuke tunanin yana nuna alamonin coronavirus, lallai ne ku killace kanku.
Ku sa ido kan alamomin. Idan suka ci gaba, sai ku nemi kulawa daga asibiti.
Alix Fox: Ya kamata mu kula da juna, kuma mu kula da kanmu. Idan kana tare da wani da yake da alamun cutar kuma kun san kun sumbaci wasu kwanan nan, ya kamata ku gaya masu. Kuma idan kun sumbaci wani sannan suka fara nuna alamu kai kuma ba ka fara nuna wa ba, sai ka killace kanka.

Bana amfani da kororon roba kafin coronavirus, ina iya farawa yanzu?

Alix Fox: Amsar wannan ya danganta da dalilin da ya sa ba ka amfani da kororon roba a baya.
Idan ba ka amfani da kororon roba ne saboda ku biyun kuna dauke da ciwon sanyi, ko kuma don kada a dauki ciki to babu damuwa.
Amma idan ba ka amfani da kororon roba ne saboda kun dogara da wasu hanyoyin hana daukar ciki kamar inzali ko kuma ba ku damu da daukar ciwon sanyi ba- lallai ne yanzu ya kamata ku yi amfani da kororon roba.
  

  

Zan iya daukar coronavirus ta hanyar taba gaban wani?

Dr Alex: Idan za ku taba gaban juna, akwai yiwuwar za ku sumbaci juna a lokaci gudan- kuma mun san cewa ana yada cutar ta miyau. Don haka, akwai yiwuwar yada cutar ta baki ko ta hannu ko ta gabanku. Muna so a rage hakan. Don haka, kada a yi mu'amala da wanda kake jima'i da shi in dai ba tare kuka zama ba.

Zan fi shiga hadarin kamuwa da coronavirus idan ina dauke da HIV?

Alix Fox: Dakta Michael Brady na Asusun Terrence Higgins ya bayar da shawara mai kyau a kan wannan. Idan kuna shan magungunan cutar HIV, kuma sinadaran CD4 (masu yaki da cutuka) da ke jikinku suna da yawa, kuma kwayoyin cutar HIV ba su da yawa a jiki, to garkuwar jikinku na da karfi kenan.
Wannan na nufin ba ka cikin hadarin kamuwa da coronavirus. Amma idan kana dauke da cutar HIV, sai ka ci gaba da shan magungunanka yadda ya kamata. Ka tabbata ka ci gaba da bin dokoki kamar yadda kowa ke yi kamar killace kai da sauransu.