Gwamnatin tarayya ta fara rabawa talakawan Abuja mutane 5000 kowanne N20,000 (Hotuna)
Gwamnatin tarayya ta kaddamar biyan kudi N20,000 ga wadanda ta siffanta matsayin yan Najeriya mafi fama da talauci 5000 a kowace jiha.
Ministar walwala, manajin annoba da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta rabawa mutanen karamar hukumar Kwali dake Abuja da kanta a ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2020.
Ta ce an kaddamar da biyan kudin ne bisa ga umurnin shugaba Muhammadu Buhari a jawabin da yayi kan sanya dokar hana fita a Abuja, jihar Legas da Ogun.
Tace: "Kamar yadda muka sani, shirin CCT na talakawa da marasa galiho ne. Wadanda suke amfana suna samun N5,000 kowani wata; amma ana biyansu N20,000 yanzu na watanni hudu."
"Za'ayi hakan a dukkan jihohin Najeriya, amma mun fara da Abuja, Legas da Ogun. Sune kan gaba (wajen yaki da cutar Coronavirus). Sauran jihohin zasu biyo baya."
"A yau muna bada N20,000 ga mutane 190 a Kwali. Mutane 5000 zasu amfana da wannan kudin a birnin tarayya Abuja."
Hajiya Sadiya ta jaddada da cewa ba'a yi son kai wajen zaben wadanda ake biya ba kuma ba yan wata jam'iyyar siyasa bane.