Idan na yi saduwa zan kamu da coronavirus? Babu mamaki kun yi wannan tunanin amma kuna kunyar tambaya. Don bambance gaskiya da karya, mun mika tambayoyinku ga kwararru. Dakta Alex George likita ne a bangaren kula ta gaggawa kuma tsohon tauraro a shirin Love Island. Alix Foz dan jarida ne a bangaren jima'I kuma tsohon mai gabatar da shirin Unexpected Fluids a tashar BBC Radio 1. Babu damuwa idan aka yi t arawa lokacin annobar coronavirus? Dr Alex George: Idan kana da aure kuma a gida daya kuke zaune babu damuwa. Amma idan wani daga cikinku na nuna alamomin coronavirus to dole ne ku rika barin tazara ko kuma ku killace kanku a cikin gidanku. Yadda ya kamata shi ne a bar tazarar mita biyu- ko a cikin gidanka amma muna ganin hakan ba zai yiwu ba. Alix Fox: Idan kana jin alamun coronavirus kadan-kadan, yana da maatukar muhimmanci kar ka yi zaton abokin zamanka (wato matarka ko mijinki) ma na fuskantar haka. Don haka, idan kana jin alamu ko yaya, ka bar tazara tsakaninka da